in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Najeriya ya lashi takwabin bunkasa kayayyakin da ake samarwa a kasar
2016-10-11 13:12:52 cri

Shugaba Muhammadu Buhari na Tarayyar Najeriya ya lashi takwabin bunkasa kayayyakin da ake samarwa a cikin kasar a wani mataki na bunkasa tattalin arzikin kasar cikin sauri.

Buhari ya bayyana hakan ne a jawabin da ya gabatar yayin bude taron kolin tattalin arzikin kasar na shekara-shekara. Yana mai cewa, ta haka ne kadai za a bunkasa galibin bangarorin tattalin arzikin kasar.

A don haka ya yi kira ga masu ruwa da tsaki, da su marawa manufofinsa game da fadada tattalin arzikin kasar baya, biyo bayan halin da kasar ta tsinci kanta a ciki.

A cewarsa, hanya daya tilo ta ginawa kasar tattalin arziki mai nagarta, ita ce karfafa kayayyakin da ake samarwa a cikin gida. Ya ce, gwamnatinsa za ta ci gaba da kokarin ganin ta cimma nasarar manufofinta na bunkasa kayayyakin more rayuwa.

Shugaba Buhari ya kuma yi fatan cewa, kwararru za su yi kwakkyawan amfani da taron na kwanaki uku wajen bullo da shawarwarin da za su kai ga magance kalubalen rayuwa da tattalin arziki da kasar take fuskanta.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China