Kakakin babban bankin Najeriya(CBN) Isaac Okorafor wanda ya bayyana hakan ga manema labarai ya ce, babban bankin kasar zai ci gaba da rage matsalar da sassan tattalin arikin kasar suke fuskanta na samun kudaden musayar ketare.
Okorafor ya kara da cewa, sashen samar da kayayyaki, da albarktun da masana'antun ke bukata, da sashen aikin gona, sune a kan gaba wajen samar da guraben ayyukan yi da kudaden shiga ga tattalin arzikin kasar.
Bayanai na nuna cewa, a watan Disamban shekarar 2016 da ta gabata, gwamnatin Najeriyar ta samar wa bangaren albarakun da masana'antu ke bukata dala miliyan 609, kana a watan Janairun shekarar 2017, sashen ya kara samun dala miliyan 228.
A bangaren kudaden musayar ketare kuwa, kakakin babban bankin kasar ya ce, a watan Disamban shekarar 2016 gwamnatin ta samarwa muhimman sassan tattalin arzikin kasar, kamar sashen samar da kayayyaki, aikin gona, da kayayyakin da ake samarwa daga gurbatatten mai da kamfanonin jiragen sama tsabar kudi har dala miliyan 1.8, baya ga karin dala miliyan 0.9 da ta samarwa wadannan sassa a watan Janairun shekarar da muke ciki.
Bugu da kari, sashen samar da kayayyakin kasar ya samu dala miliyan 53 da kuma wasu karin dala miliyan 71 a wadannan lokuta da muke magana akai.(Ibrahim)