in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Majalisar Dattijan Nijeriya ya ce Sahihin kasafin kudi zai inganta tattalin arzikin kasar
2017-02-14 09:48:35 cri

Shugaban Majalisar Dattijan Nijeriya Bukola Saraki, ya ce tasirin sahihin kasafin kudi kan tattalin arzikin kasar, abu ne da ba zai misaltu ba.

Bukola Saraki ya bayyana haka ne jiya Litinin a Abuja, babban birnin kasar, yayin bude taron jin ra'ayoyin jama'a kan da kasafin kudin kasar na bana, da kwamitocin majalisar dattijan da takwararta ta wakilai masu kula da batun kasafin kudi suka shirya.

Ya bayyana cewa, babbar matsalar a koda yaushe ita ce, aiwatar da kasafin yadda ya kamata, wanda shi ne ginshikin raya tattalin arziki.

Saraki ya ce tsarawa da aiwatar da kasafi yadda ya dace, hanyoyi ne da za su taimakawa gwamnati samar da abubuwa da za su inganta zamantakewa da tattalin arziki ta yadda kowa zai amfana.

Ya kara da cewa, hanya mafi dacewa ta cimma wannan manufa ita ce, tuntubar masu ruwa da tsaki yayin da ake daukar matakai ko yanke shawara, musamman kan batutuwan da suka shafi al'umma kai tsaye.

Shugaban majalisar dattijan ya kuma tabbatar da cewa, majalisar dokokin tarayya a shirye take, ta taimaka wa bangaren zartawa a kokarinta na samar da ci gaban da ake muradi. ( Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China