Mai Magana da yawun babban bankin Najeriya CBN Mr. Isaac Okorafor, ya ce bankin na Najeriya, zai ci gaba da daukar dukkanin matakan da suka wajaba, domin tabbatar da daidaito a kasuwar canjin kudin kasar.
Cikin wata sanarwa da ya fitar, Mr Okorafor ya ce bankin na CBN na shirin daukar karin matakai, na ganin ya dakile matsalar karancin kudaden canji na kasashen waje da ake fama da ita, ta yadda masu bukatun wadannan kudaden na hakika, na samun su cikin sauki a kuma farashi madaidaici.
Jami'in ya kara da cewa CBN zai tabbatar da karya lagon masu yiwa shirin sa kafar ungulu, ta hanyar kara yawan dalar Amurka da yake samarwa bankuna, matakin da zai kai ga wadatar kudaden musayar ga 'yan kasa. Har ila yau bankin zai kara adadin kudaden canjin da yake baiwa masu sana'ar canji daga dala 8,000 zuwa dala 10,000 a ko wane mako.
Daga nan sai ya ja hankalin bankunan cinikayyar kasar, da su kauracewa duk wani mataki, da ka iya zama tarnaki ga manufar gwamnati, ta samar da kudaden canji cikin sauki ga al'ummar Najeriya.(Saminu Alhassan)