A wata sanarwar da hukumar gudanarwa ta yawon bude ido ta kasar Sin ta sanar a jiya Talata, ta ce ta samu kudaden shigar daga masu yawon bude ido na cikin gida miliyan 93.
Ita dai ranar sharar kaburbura, wanda aka fi sani da Qingming Fesfival, biki ne mai matukar muhimmanci ga al'ummar Sinawa, domin nuna girmamawa ga magabata. Mafi yawan Sinawa kan shafe hutun na kwanaki uku suna gudanar da tafiye tafiye da sharar kaburbura.
Mafi yawa daga cikin masu yawon shakatawar sun gudanar da zirga zirga ne ta hanyoyin mota. Bugu da kari, wasu fasinjojin da yawansu ya kai miliyan 35 sun gudanar da zirga zirgar ne ta jiragen kasa, kuma galibinsu sun ziyarci biranen Beijing, Tianjin, Hebei, da kuma yankunan kogin Yangtze ne.
Fannin yawon bude ido na kasar Sin ya kasance wani muhimmin bangare ga kasar saboda gudanar da ayyukan hidima da samun karuwar tattalin arziki , kana yana da matukar amfani wajen cimma muradun abokan hulda. (Ahamd Fagam)