in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Al'ummar Masar sun gudanar da bikin Sham El-Nessim, duk da jimamin hare-haren da aka kai kasar a makon jiya
2017-04-18 10:13:04 cri
Miliyoyin al'ummar kasar Masar ne suka gudanar da bikin Sham El-Nesim a jiya Litinin, wanda ake yi a fadin kasar don shigar yanayin bazara, duk da alhinin da suka shiga sanadiyyar munanan hare-haren da aka kai kan mujami'u a makon da ya gabata.

Da sanyin safiyar jiyan ne Musulmai da kiristoci suka taru a wuraren shakatawa, da suka hada da bakin ruwa da gidajen adana namun daji da sauransu, a daidai lokacin da aka tsaurara matakan tsaro a fadin kasar.

Ba tare da la'akari da addini ko akida ko matsayi ba, al'ummar kasar kan yi bikin wannan rana ta Sham El-Nessim wanda ke nufin 'shigowar bazara' tun a shekarun 2700BC, inda ake cin abincin gargajiya da fita shakatawa.

Wannan rana a bana, na zuwa ne mako guda bayan an kai hare-haren kunar bakin wake a wasu mujami'u biyu a Lardin Delta dake Gharbiya da Lardin Alexandria dake arewacin kasar, al'amarin da ya yi sanadin mutuwar a kalla mutane 45 yayin da wasu 120 suka jikkata.

Wani direban tasi Moustafa Ahmad da ya fita shakatawa da iyalinsa, ya ce al'adar al'ummar kasar ne kaunar juna da jin dadin rayuwa ba tare da la'akari da kalubalen da suke ciki ba.

Moustafa Ahmad wanda ya ce a ranar Musulmai da kiristoci kan yi murna a tare, ya ce sun fuskanci matsaloli da dama, kuma sun yi bakin ciki da asarar rayuka da aka yi sanadiyyar hare-haren.

Har ila yau, ya ce Sham El-Nessim lokaci ne na sake sabuwar rayuwa, kuma harin ta'addanci ba zai yi wa jin dadinsu tarnaki ba. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China