in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Babbar jami'ar kasar Sin ta gana da ministan harkokin fasaha da al'adun Afirka ta Kudu
2017-04-24 20:44:35 cri

A yau Litinin ne agogon birnin Pretoria na kasar Afirka ta Kudu, mataimakiyar firaministan kasar Sin madam Liu Yandong ta gana da ministan harkokin fasaha da al'adun kasar Afirka ta Kudu Nathi Mthethwa, kana shugaban kwamitin kula da tsarin tsarin musayar al'adu tsakanin kasashen Sin da Afirka ta kudu, gabanin taro karo na farko game da tsarin musayar al'adu tsakanin kasashen Sin da Afirka ta kudu.

A yayin ganawar, madam Liu ta ce, tsarin musayar al'adu tsakanin kasashen Sin da Afirka ta kudu, shi ne irin tsari na farko a tsakanin Sin da kasashen Afirka, wanda ba kawai zai kyautata amincewa da juna da kara dankon zumuncin da ke tsakanin jama'ar Sin da Afirka da Kudu ba, har ma zai kasance abin misali wajen inganta mu'amala tsakanin Sin da kasashen Afirka baki daya. A saboda haka,kamata ya yi kasashen 2 su raya yin mu'amala a tsakanin Sin da Afirka ta Kudu ta fuskar al'adun jama'a ta yadda zai zama abin koyi wajen yin mu'amala tsakanin Sin da Afirka ta fuskar al'adun da raya huldar abokantaka da ke tsakaninsu daga dukkan fannoni bisa manyan tsare-tsare zuwa sabon mataki, a kokarin ba da gudummowa cikin himma don kara inganta hadin gwiwa a tsakanin kasashen Sin da Afirka, da kasashen Asiya da Afirka,da kuma tsakanin kasashe masu tasowa.

A nasa bangaren, Nathi Mthethwa ya ce, kafa tsarin musayar al'adu tsakanin kasashen Sin da Afirka ta kudu zai taimaka wajen kyautata dankon zumunci da ke tsakanin jama'ar Afirka ta Kudu da Sin, da inganta hadin gwiwa a tsakanin kasashen 2 a fannonin kimiyya da fasaha, ba da ilmi, al'adu, harkokin yawon shakatawa da dai sauransu. Ya kuma yi imani da cewa, tsarin zai taka muhimmiyar rawa wajen kara bunkasa huldar abokantaka da ke tsakanin Afirka ta Kudu da Sin daga dukkan fannoni bisa manyan tsare-tsare da kara bunkasa hadin kai tsakanin kasashe masu tasowa. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China