Taron wanda ya gudana a jiya Alhamis, a birnin Johannesburg na kasar Afirka ta Kudu, ya samu halartar wakilai daga bangarorin siyasa, da na cinikayya, da hada-hadar kudi na Sin da na Afirka ta Kudu fiye da 100, inda suka tattauna game da makomar hadin gwiwa tsakanin kamfanonin Sin da na Afirka.
Wannan dandalin tattaunawa dai ya zamo daya daga cikin manyan ayyuka game da kasar Sin, wanda aka gudanar a kasar Afirka ta Kudu.
An dai raba tattaunawar gida biyu, inda kashi na farko ya kunshi harkokin ma'adinai da karafa, da kuma fanni na biyu wanda ya mai da hankali kan harkokin sana'o'i daban daban.
Makasudin dandalin tattaunawar dai shi ne bayyanawa kamfanonin Sin irin damar dake akwai a fannonin zuba jari a Afirka ta Kudun, da kuma bayyanawa gwamnatin kasar Afirka ta Kudu, da kamfanonin kasar bukatun zuba jari, da fasahohin kamfanonin kasar ta Sin. Ana kuma fatan hakan zai samar da karin fahimtar juna tsakanin kamfanonin Sin da na Afirka ta Kudu, ya kuma aza janyo hankalin kamfanonin Sin su zuba jari a Afirka ta Kudu, tare da bude sabon babin hadin-gwiwa a tsakaninsu da kamfanonin Afirka ta Kudu. (Zainab)