Babban daraktan madaba'ar Li Jianguo ne ya bayyana hakan, ya yin zantawar sa da wakilin kamfanin dillancin labaru na Xinhua. Ya ce baya ga littattafai, za su samar da mujallu da shafukan yanar gizo, domin samar da karin bayanai game da kasar Sin.
Mr. Li ya kara da cewa sun samu matukar kwarin gwiwa daga masu karatu, a yayin bikin baje kolin littattafai da suka halarta a birnin Johannesburg, tsakanin ranekun 31 ga watan Yuli zuwa 2 ga watan nan na Agusta.
Ya ce a matakin farko madaba'arsa za ta samar da littattafai game da tarihin kasar Sin, da yarukan ta, da rubuce-rubucen bincike, da na sassan ilimi, da ci gaban al'adu da tattalin arziki. A cewar sa za su yada wadannan littattafai ne kasancewar Sin kasa ce da a yanzu ke kara yin fice a idon duniya.
Kaza lika jagoran na CIPG ya ce kyakkyawar dangantakar dake tsakanin Afirka ta kudu da Sin, ta sanya mutane da dama maida hankali ga neman sanin tarihi da yarukan kasar Sin.(Saminu Alhassan)