Yayin zantawar tasu Xi Jinping ya jaddada cewa, kamata ya yi kasashen Sin da Amurka su aiwatar da ayyukan da suka cimma daidaito a kan su, da sa kaimi ga bunkasar dangantaka tsakaninsu yadda ya kamata. Kana bangarorin biyu su kara yin mu'amala da juna, da gudanar da aikin shirya ziyarar shugaba Trump a kasar Sin ta bana, da shirya yin shawarwari kan harkokin waje, da fannin tattalin arziki, da dokoki, da tsaron yanar gizo, da zamantakewar al'umma, da al'adu da sauransu a tsakanin kasashen biyu cikin hanzari.
Kaza kika a sa kaimi ga hadin gwiwar sassan biyu a fannonin tattalin arziki da cinikayya, da aikin soja, da kula da dokoki, da tsaron yanar gizo, da musayar al'adu, da lura da kananan gwamnatoci da sauransu. Sai kuma fannin kara mu'amala da juna kan batutuwan kasa da kasa da na shiyya-shiyya, da daga dangantakar dake tsakanin kasashen biyu zuwa wani sabon matsayi.
A nasa bangare, shugaba Trump ya nuna gamsuwa ga bunkasuwar dangantakar dake tsakanin kasashen biyu, yana mai jinjinawa jama'ar kasar Sin. Ya ce, yana da muhimmanci sosai a kiyaye mu'amala kan manyan batutuwan dake shafar sassan biyu.
Haka zalika kuma, shugabannin kasashen biyu sun yi musayar ra'ayoyi kan halin da ake ciki a zirin Koriya. Game da hakan Xi Jinping ya jaddada cewa, Sin tana adawa da duk wani aiki na sabawa kudurorin kwamitin sulhun MDD, tare da fatan bangarori daban daban da abin ya shafa za su kai zuciya nesa, su kaucewa ta da zaune tsaye da tsananta halin da ake ciki a zirin.
Har ila yau Sin tana fatan ci gaba da kokari tare da bangarori daban daban da abin ya shafa, ciki har da kasar Amurka, wajen kiyaye zaman lafiya a zirin Koriya, da arewa maso gabashin Asiya, har ma a dukkan duniya. (Zainab)