in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Xi Jinping ya zanta da Trump ta wayar tarho
2017-04-12 13:51:15 cri

Da safiyar yau Laraba ne shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya zanta da shugaban kasar Amurka Donald Trump ta wayar tarho, inda Xi ya jaddada cewa, ganawar da suka yi 'yan kwanaki a kasar Amurka ta haifar da babban sakamako, kuma al'ummar kasar Sin da al'ummomin kasashen duniya na jinjinawa sakamakon matuka.

Xi ya yi nuni da cewa, yayin ganawar, sun yi musayar ra'ayoyi kan huldar dake tsakanin kasashen Sin da Amurka a halin yanzu, da sauran manyan batutuwan dake shafar kasa da kasa, da kuma shiyya shiyya wadanda suka cimma ra'ayi daya kan su.

Ya ce, shugabannin biyu sun kara zurfafa fahimtar juna tsakanin su, yayin da a nan gaba kuma, sassan biyu wato Sin da Amurka za su aiwatar da tsarin shawarwari a fannoni hudu, wato diplomasiyya, da tattalin arziki, da shari'a, da kuma al'adu, domin tabbatar da shirin tattaunawar ciniki cikin kwanaki 100 masu zuwa.

A nasa bangare, Trump ya bayyana cewa, ya yi farin ciki kwarai, bisa ganawar sa da shugaba Xi tare da samun babban sakamako. Kuma nan gaba, kamata ya yi shugabannin kasashen biyu su kara yin cudanya, tare kuma da karfafa hadin gwiwa dake tsakanin kasashensu, domin samun ci gaba tare.(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China