in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaba Xi Jinping ya gana da jagorar gwamnatin yankin Hong Kong
2017-04-11 20:09:15 cri

Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya gana da sabuwar jagorar yankin Hong Kong mai cin gashin kan sa Lam Cheng Yuet-ngor a Talatar nan, yayin taron tattauna kan batutuwan shugabanci da ya gudana a fadar Zhongnanhai dake tsakiyar birnin Beijing.

Yayin ganawar ta su, shugaba Xi ya taya Lam murnar lashe zaben yankin Hong Kong da aka gudanar, inda ta zamo shugabar yankin ta 5 a tarihi. Kaza lika shugaban na Sin ya tabbatar mata da cewa, ta dace a duk wasu sharuddan jagoranci da ake bukata.

Shugaba Xi ya kara da cewa, cikin shekaru 36 da ta kwashe tana ayyukan hukuma, ciki hadda mukamai daban daban da ta rike a yankin na Hong Kong, Lam ta nuna kwarewa da sanin makamar aiki, da kaunar kasa da yankin na Hong Kong, ga kuma iya warware lamurra masu sarkakiya.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China