Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya nuna bukatar kara inganta hadin gwiwa tsakanin kasar sa da Sao Tome da Principe. Shugaban na Sin ya bayyana hakan ne yayin da ya karbi bakuncin Firaministan Sao Tome da Principe Patrice Trovoada a nan birnin Beijing a yau Juma'a.
Shugaba Xi ya ce ya zama wajibi kasashen biyu su daga matsayin dangantakar su, ta yadda za su ci gajiyar al'amura da suka shafe su, da ma sauran al'amura na kasa da kasa.
Ya ce alakar Sin da Sao Tome da Principe ta shiga wani sabon babi, tun bayan da sassan biyu suka amince da tsari mafi dacewa da zamani. A kuma wannan gaba, Sin na jinjinawa gudummawar da Mr. Trovoada ya bayar wajen kyautata alakar kasar sa da Sin.
Daga nan sai shugaban na Sin ya alkawar ta cewa, kasar sa za ta ci gaba da hadin kai da Sao Tome da Principe a dukkan sassa na ci gaba, tare da kafa wani tsari mai fadi cikin daidaito, da martaba juna, tare da cin gajiya ta bai daya tsakanin ta da Tome da Principe.
A nasa bangare kuwa, Mr. Trovoada cewa ya yi, sake maido da alaka tsakanin kasar sa da Sin, mataki ne da ya samu matukar amincewa daga al'ummar kasar sa, kuma za su ci gaba da goyon bayan manufar kasar Sin daya tak a duniya.(Saminu Alhassan)