in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Iran ta yi kira da a gudanar da taro tsakanin masu daddale yarjejeniyar nukiliya ta Iran
2016-12-18 13:58:22 cri
Ministan harkokin waje na kasar Iran Mohammad Javad Zarif ya aika da wasika zuwa ga ministan harkokin waje na kungiyar tarayyar Turai Federica Mogherini, inda ya bukaci a kira taro a tsakanin bangarorin da suka sa hannu kan yarjejeniyar nukiliyar Iran, don a sa ido game da yadda ake aiwatar da yarjejeniyar, ta yadda za a daidaita batun tsawaita dokar kakaba wa Iran takunkumi da kasar Amurka ta yi, aikin da ya keta yarjejeniyar.

A wasikar da ya aike da ita, Mohammad Javad Zarif ya ce, a shekara guda da rabi da ake aiwatar da yarjejeniyar, Iran ta cika alkawuran da ta dauka, sai dai yarjejeniyar na bukatar kokari daga bangarori daban daban. Domin ganin yarjejeniyar ta ci gaba da taka rawar da ta dace, dole ne masu daddale ta su ci gaba da cika alkawuran da suka dauka.(Lubabatu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China