A wata sanarwar da ma'aikatar harkokin wajen ta Najeriyar ta gabatarwa kamfanin dillancin labarai na Xinhua, tace harin da aka kaddamar kwanan nan a tashar mota ta Polokwane dake lardin Limpopo kasar a Afrika ta kudun, inda ya rutsa da wasu yan Najeriya biyu, ba za'a lamunta ba.
Ko da yake ma'aikatar tace wannan hari ba shi da alaka da nuna kyamar baki, kuma babu hasarar rayuka ba a harin na baya bayan nan, sai dai kuma lamarin ya faru ne kwanaki kadan bayan da tawagar gwamnatin tarayya suka gudanar da zama na musamman da mahukunta kasar Afrika ta kudun da wakilan majalisun dokoki na kasasshen biyu cikin nasara wanda ya gunada a Afrika ta kudun.
Sanarwar ta kara da cewa, mai rikon mukamin jakadan Najeriya a Afrika ta kudun, Martin Cobham, yana cigaba da yin aiki tare da hadin gwiwar karamin jakadan kasar a Johannesburg Godwin Adama, tare da hadin gwiwar 'yan Najeriyar mazauna Afrika ta kudu da masu ruwa da tsaki daga mahukuntan kasar Afrika ta kudu don magance rikicin cikin ruwan sanyi.