in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
ANC ta yi alkawarin magance kalubalen da take fuskanta
2017-03-13 10:08:13 cri
A jiya Lahadi ne Jam'iyyar ANC mai mulki a kasar Afirka ta kudu ta kaddamar da wasu manufofinta, inda ta lashi takwobin magance tarin kalubalen cikin gida da jam'iyyar take fuskanta a halin yanzu.

Kundin jam'iyyar ya gano cewa, yanzu haka dai jama'a na kara dawowa daga rakiyar jam'iyyar, yayin da jam'iyyar ta kasa tabuka abin a zo a gani a zabukan kananan hukumomi na shekarar da ta gabata da kuma yadda jama'a ke ci gaba da sukarta.

Idan ba a manta ba jam'iyyar ANC ta rasa manyan birane kamar Johannesburg da Pretoria da mazabar Nelson Mandela Bay. Baya ga zarge-zargen da ake yi wa jam'iyyar na nuna rashin girmama mutane da cin hanci da rashawa da nuna wariya da kuma uwa uba gazawa wajen sauke nauyin da jama'a suka dora mata.

Saboda haka, ANC ta ce, muddin tana son cimma burin da ta sanya a gaba, wajibi ne ta gaggauta dawo da martabarta a idon jama'a, ta yadda za ta kasance jagorar canji. (Ibrahim Yaya)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China