Mai tsawatarwa na marasa rinjaye a Majalisar, Muhammad Muntaka Mubarak, ya yi kira ga sauran kasashen Afrika, su daina amfani da kayakin da ake sarrafawa a kasar Afrika ta Kudu, al'amarin da zai nunawa kasar rashin jin dadinsu game da harin da ake kai wa al'umomin kasashensu.
Da yake jawabi a wani gidan rediyo, daya daga cikin mambobin majalisar Samuel Okudzeto Ablakwa ya yi kira ga Tarayyar Afrika AU, ta sa baki cikin lamarin, yana mai cewa, hare-haren ka iya barazana ga tsaro da bunkasar tattalin arzikin nahiyar.
Amma a jiya Juma'a, Ministar harkokin wajen Ghana Shirley Ayorkor Botchwey, ta shaidawa majalisar dokokin cewa, biyo bayan hare-haren na kin jinin baki da ya barke a wasu sassa na Afrika ta Kudu, ma'aikatarta ta dauki matakan tabbatar da tsaron lafiyar 'yan asalin Ghana dake zaune a kasar.
Ta ce zuwa yanzu, babu wani dan kasar Ghana ko harkokin kasuwanci 'yan kasar da hare-haren suka shafa, ta na mai cewa, ofishin Jakadanci Ghana dake Pretoria da ma'aikatar harkokin wajen, za su ci gaba da bibiyar lamarin, tare da yi wa kasar karin bayani yadda ya kamata. ( Fa'iza Mustapha)