Jagoran wakilan Rasha, kuma wakilin musammam na Shugaban kasar ka rikicin Syria Alexander Lavrentiev, ya ce ba su ji dadin rashin halartar bangaren adawar Syria ba. Sai dai ya ce a ganinsu, kawai kirkirar uzuri suka yi.
An fara zagaye na uku na taron neman sulhu kan rikicin Syria a Astana babban birnin Kazakhstan ne a jiya Talata, inda ake gudanar da taron ta hanyar tuntubar bangarori biyu na kasar da sauran masu ruwa da tsaki.
Ana sa ran a gudanar da wani zaman taron a yau Laraba 15 ga watan Maris. (Fa'iza Mustapha)