in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasashe masu saurin bunkasuwar tattalin arziki sun ba da babbar gudummawa wajen raya tattalin arzikin duniya
2017-03-18 17:24:04 cri
Mataimakin shugaban Asusun ba da lamuni na IMF Zhang Tao, ya bayyana a yau Asabar cewa, ana fuskantar yanayi mai kyau wajen raya tattalin arzikin duniya, kuma kasashe masu saurin bunkasuwar tattalin arziki sun ba da gudummawa matuka wajen inganta bunkasuwar tattalin arzikin duniya gaba daya, wadanda suka ba da gudummawar kashi 70 bisa dari a wannan fanni, musamma ma kasashen Sin, da Indiya da wasu kasashen dake nahiyar Asiya, za su ci gaba da jagorantar karuwar tattalin arzikin duniya.

Mr. Zhang, ya bayyana haka ne a yayin taron dandalin tattaunawar bunkasuwar kasar Sin na shekarar 2017. Haka kuma, ya ce, bisa hasashen da Asusun IMF ya yi, an ce, adadin karuwar tattalin arzikin duniya zai kai kashi 3.4 bisa dari a bana, yayin da adadin zai kai kashi 3.6 bisa dari cikin shekara mai zuwa, sabo da farfadowar yanayin bunkasuwar tattalin arzikin duniya. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China