Ma'aikatar cinikayya da kwamitin bunkasa kasa tare da samar da sauye sauye na kasar, wadanda su ne suka tsara ta, sun ce dokar za ta fayyace ka'idojin zuba jari a kasashen ketare da ma yankuna, tare da lasafta masana'antun da kamfanonin da gwamnatin kasar Sin za ta baiwa goyon baya, da ma wadanda za a ki amincewa da su.
Sabuwar dokar dai za ta hade sassan tsare tsare da ake da su a baya a wannan fanni, ciki hadda tsarin samun amincewar gwamnati, da na hada hadar kudi, da na lura da riba da kuma batun haraji.
Rahotanni na nuna cewa fannonin da za a fi karfafawa su ne wadanda suka shafi bunkasa jin dadin jama'a, da raya tattalin arziki, musamman masu alaka da cimma nasarar manufar nan ta ziri daya da hanya daya, yayin da kuma za a dakile zuba jari a sassan da ba su da wata cikakkiyar moriya.
Kaza lika dokar za ta tanaji hukunci, ga duk wadanda suka karya dokokin zuba jari a cikin kasar ta Sin da ma na kasashen waje. (Saminu Hassan)