Mamabobin majalisar sun amince cewa cinikayya ta Intanet ta zama wata babbar hanyar habaka tattalin arziki, kuma samun ci gaba da harkar ya yi cikin sauri, ya bada gagarumar gudunmuwa ga ci gaban tattalin arziki, samar da aikin yi da kuma zamantakewar al'umma.
Sai dai, sun kara da cewa, har yanzu ana fuskantar matsaloli da suka hada da sayar da kayakin jabu, take dokar hakkin fasaha, tallar karya da kuma rashin tabbatar da tsaron bayanan masu sayen kayayyaki.
Wasu daga cikin mashawartan sun yi kira da a gaggauta samar da dokokin daidaita harkar ta yadda zai samun inganci, sannan a inganta shigar da fasahar sadarwa, tare da nazarin matsaloli da za a iya fuskanta yayin da ake samun ci gaba.
Sun kuma bada shawarar fayyace hakkokin hukumomin gwamnati da cibiyoyi masu cinikayya ta Intanet, suna masu cewa ya kamata gwamati ta mara baya tare da tabbatar da bunkasar cibiyoyin, yayin da su kuma cibiyoyin za su sauke dukkan nauyin da ya rataya a wuyansu wajen kare bayanan masu cinikayya da su. (Fa'iza Mustapha)