Kakakin ma'aikatar harkokin cikin gida ta kasar Faransa Pierre-Henry Brandet ya bayyanawa 'yan jarida a wannan rana cewa, an kaiwa 'yan sandan hari ne da gangan. Yanzu haka Ana kokarin tabbatar da asalin wanda ya kai harin, watakila akwai masu taimaka masa, 'yan sanda dai suna kokarin yin bincike game da musababin harin.
Kungiyar IS ta sanar da daukar alhakin kai harin ta hanyar kamfanin dillancin labaru na Amaq, tana mai cewa maharin dan kasar Belgium mamban kungiyar ne.
A jawabin da ya gabatar shugaban kasar Faransa François Hollande ya bayyana cewa, tuni mai gabatar da kara na kasar ya fara yin bincike kan batun. Ya ce, hukumomin kasar za su kara mai da hankali kan abubuwan da ke gudana a yayin babban zaben da za a yi a kasar. (Zainab)