Wata sanarwa da kakakin hukumar ta DSS Tony Opuiyo ya fitar a jiya, ta ce bayan gudanar da bincike, hukumar ta kama mayakan Boko Haram guda biyar dake da alaka da kitsa harin.
Tony Opuiyo ya ce an kama mutanen ne a jihar Benue dake arewa maso tsakiyar kasar cikin watan Maris din da ya gabata.
Gwamnatin Nijeriya dai ta samu gagarumar nasara a yaki da take da kungiyar Boko Haram, inda cikin watan Disamban da ya gabata, jami'an tsaro dake aiki a yankin da ayyukan kungiyar ya fi kamari, suka fattakin 'ya'yan kungiyar daga dajin Sambisa da ya kasance tungarsu. (Fa'iza Mustapha)