A kwanan nan ne, gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta yanke shawarar yaki da cin hanci ta hanyar amfani da masu tsegumi a matsayin wata sabuwar dabara.
Wannan mataki, zai ba jama'a damar bada rahoto ta wata kafa cikin sirri, inda za su samu wani kaso daga cikin kudaden da aka kwato.
Masu tsegumin za su samar da bayanai ga hukumomi kamar EFCC mai yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasa tu'annuti, ta yadda za su taimaka musu wajen kwato kudaden gwamnati da aka yi sama da fadi da su.
Laifukan da za a iya kai rahotonsu sun hada da sace kudade da kadarorin gwamnati, da take ka'idojin hada-hadar kudade, da neman na goro da kuma sauya bayanai.
Idan har tsegumin ya kai ga nasarar samo kudaden da aka yi sama da fadi da su, to wanda ya tseguntawa hukumomi zai samu tukwicin tsakanin kashi 2.5 zuwa kashi 5 na kudin.
Gwamnatin dai ta yi alkawarin tabbatar da kare sirrin masu tsgeunta mata kamar yadda doka ta tanada.
Zuwa yanzu dai, dabarar ta tseguntawa hukumomi na aiki a Nijeriya. (Fa'iza Mustapha)