Cikin wata sanarwa da ya fitar jiya Talata, Ministan yada labarai da al'adu na kasar Lai Muhammad, ya tabbatar da cewa, gwamnatin ta daukaka dukkan shari'o'in a matakin kotun daukaka kara, inda za ta yi binciken kwa-kwaf kan shari'o'in.
Lai Muhammad ya ce ana sake nazari na tsanaki kan hukunce-hukuncen, domin tantance ko matsalar tana daga bangaren gwamnati, ko kuma kokarin mai da ta abun wasa ake yi.
Ya ce yaki da cin hanci da rashawa abu ne mai wahala kuma zai shafe lokaci mai tsaho, amma gwamnati ta shirya tsaf don tunkarar aikin.
Har ila yau ya kara da cewa, dole ne gwamnati ta yi nasara domin ka'idojin doka da jama'a na mara mata baya, yana mai cewa, somin tabi kawai aka yi, don haka, babu wani abu da zai dauke hankalinta koma ya sanyaya mata gwiwa. (Fa'iza Mustapha)