Mahamudu Bamuwai ya ce Ghana ta kasance kasa mai cike da tsaro a yankin mashigin ruwan Guinea da ya fi ko ina fuskantar matsolilin bata gari a tekuna a fadin duniya.
Ya kara da cewa, kasarsa ta kuduri niyyar taimakawa makwaftan kasashe samun zaman lafiya da kwanciyar hankali, la'akari da cewa, duk abun da ya faru a yankin, zai iya tasiri ga sauran kasashe makwafta.
Mataimakin shugaban kasar na Ghana na wannan bayani ne yayin wani taron nahiyar Afrika karo na 3, matakan sanya ido a gabobin ruwa da baje kolin ayyukan Soji da ya gudana a Accra babban birnin kasar.
Taron ya samu halartar kwararru da masana kan tsaron gabar ruwa daga fadin duniya, inda suka tattauna kan hanyoyin magance barazana da tsaron gabobin ruwa ke fuskanta. (Fa'iza Mustapha)