in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ghana ta fara shirin dashen itatuwa
2017-03-22 10:26:31 cri
A jiya Talata kasar Ghana ta sanar da fara shirinta na inganta gandun daji, tare da bullo da taron dandalin zuba jari na (FPIF) don farfado da shirin dashen bishiyoyi a kasar.

Dandalin wanda ke da mambobi 15, ya kunshi wakilai daga jahohi da masu ruwa da tsaki a fannin gandun daji da suka hada da kungiyoyi da bana gwamnati ba na cikin gida dana kasa da kasa.

Da yake kaddamar da dandalin don tunawa da ranar gandun daji ta duniya shekarar 2017, babban jami'in hukumar kula dazuzzuka ta kasar Ghana, Kwadwo Owusu Afriyie, ya bukaci kwamitin mai mutane 15 da su yi iyakacin kokarinsu wajen ganin cewa an samar da isassun kudaden da hukumar zata gudanar da al'amurranta yadda ya kamata.

Tun bayan kaddamar da shirin kula da gandun daji dana dabbobin daji na shekarar 2012, kana da kaddamar da shirin inganta dazuka na Ghana na shekarar 2016 zuwa shekarar 2040 a watan Nuwambar 2016, yace ya zama dole a dauki kwararan matakai domin aiwatar da shirin kamar yadda yake kunshe cikin daftarin domin cimma burin da aka sanya gaba.

Jami'in ya bukaci mambobin na FPIF, da su sauke nauyin da aka dora musu wajen samar da yanayin da zai dace da cin moriyar shirin daga dukkan sassa na masu ruwa da tsaki a kasar.

FPIF an dora musu manyan ayyuka biyu da suka hada da lalibo hanyoyin da za su ja hankulan masu zuba jari da kuma kokarin samar da kyakkyawan yanayin zuba jari a fannin raya dazuka, wanda ta haka ne za'a cimma burin da aka sanya gaba.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China