Kumbon na Tianzhou-1, shi ne irinsa na farko da kasar Sin ta harba, matakin da zai taimaka wajen bunkasa shirin kasar na kafa tashar sararin samaniya ta bincike mallakar kasar ta Sin nan da shekara ta 2022.
An dai yi amfani da rokar Long March-7 wajen harba kumbon na Tianzhou-1, kamar dai yadda aka tsaya hakan tun da farko. Da zarar ya isa sararin samaniya kuma, kumbon zai hade da kumbon Tiangong-2 dake kunshe da dakin binciken kimiyya, ya kuma samu karin makamashi da sauran kayan aiki da yake bukata. Kaza lika za a yi amfani da shi wajen gudanar da binciken kimiyyar sararin samaniya kafin dawowarsa doron kasa.
Sin dai na da nufin kafa tashar dindindin ta sama jannati mallakar kasar wadda za ta zamo na kewaye kan falakin ta har tsawon shekaru 10, kuma harba sabon kumbon Tianzhou-1, daya ne daga matakan cimma wannan buri. (Saminu Hassan)