An dai yi gwajin jirgin mai saukar ungulu ne yayin wani ruwan sama kamar da bakin kwarya, a birnin Jingdezhen dake lardin Jiangxi a gabashin kasar Sin ranar Juma'ar da ta gabata.
A cewar jami'an kamfanin Changhe, wanda ya kera jirgin, samfurin na AC313 na iya tashi da sauka a yayin ruwan sama mai tsanani, wanda hakan ke nufin za a iya aiki da shi a yayin ayyukan ceto, da na kashe wutar daji, ko sufurin jama'a. Kaza lika zai dace da ayyukan bada agajin lafiya, da yawon bude ido, da kuma zirga zirgar kasuwanci. (SaminuHassan)