Kunbon na dakon kaya mai lakabin Tianzhou-1, tuni ya bar birnin Tianjin dake arewacin kasar, zuwa tashar harba kumbuna dake Wenchang a lardin Hainan, inda ake sa ran harhada shi, tare da yin gwaje gwajen da suka wajaba.
Harba kumbon Tianzhou-1, zai kasance daya daga manyan matakan da Sin ke dauka, a shirinta na kafa tashar binciken sararin samaniya nan da shekara ta 2020. Tianzhou-1 zai yi dakon muhimman kayayyaki da ake bukata domin cimma nasarar kafa wannan tasha. (Saminu Hassan)