A jiya Litinin ne kwararru dake aikin bincike a sassan teku na kasar Sin, suka fara wani bincike irin sa na 38, a yankunan teku masu zurfi ta hanyar amfani da jirgin ruwan dake iya tafiya a karkashin teku mai suna Jiaolong.
Aikin wadanda masu binciken za su gudanar tsakanin ranekun 6 ga watan nan na Fabarairu zuwa 9 ga watan Yuni mai zuwa, zai kasance irin sa mafi tsayi da masanan za su gudanar a tarihi.
Tuni dai babban jirgin dako na Xiangyanghong 09 mai dauke da Jiaolong, ya bar tashar ruwan birnin Qingdao dake gabashin kasar Sin dauke da masu bincike 150 domin wannan aiki na kwanaki 124.
Ana sa ran masu binciken za su gano sabbin abubuwa da bayanai game da ruwayen arewa maso yammacin tekun Indiya, da tekun kudancin Sin, da zirin tekun Yap da Mariana wadanda ke yankin tekun Fasifik, kamar dai yadda jagoran shirin Han Xiqiu ya bayyana.(Saminu)