in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin za ta yi kokarin ciyar da hadin gwiwarta da waje a fannin kimiyya da fasaha
2017-01-10 13:13:44 cri

A jiya Litinin ne, mataimakiyar firaministar kasar Sin Liu Yandong ta gana da wasu kwararru a fannin kimiyya da fasaha daga kasashen Jamus, Amurka, Faransa, wadanda suka lashe lambar yabo a fannin hadin gwiwar kimiyya da fasaha ta shekarar 2016 da kasar Sin ta bayar.

Yayin da ta ke ba su lambobin, Madam Liu Yandong ta taya su murnar lashe lambar yabon a madadin gwamnatin kasar Sin,tare da nuna musu godiya bisa ga babbar gudummawar da suka bayar ga bunkasuwar sha'anin kimiyya da fasaha na kasar Sin da ci gaban rayuwar bil Adama.

Bugu da kari, Madam Liu ta kara da cewa, gwamnatin kasar Sin za ta himmatu wajen shiga a dama da ita a tsarin kirkire-kirkire na duniya, da kyautata tsarinta na bude kofa ga kasashen waje da hadin gwiwa tare da sauran kasashen duniya a fannin kimiyya da fasaha, a kokarin samar da kyakkyawan muhalli ga aikin shigo da kwararrun ketare zuwa kasar Sin don yin aiki da kuma cudanya, ta yadda za a kara samun ci gaban masana'antun kimiyya da fasaha ta hanyar hadin kan Sin da kasashen waje.(Kande Gao)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China