A tsakar ranar jiya, firayin ministan kasar Sin Li Keqiang wanda ke yin ziyarar aiki a kasar New Zealand da takwaransa na kasar ta New Zealand Bill English sun halarci liyafar da aka shirya musamman ma domin maraba da zuwansa a kasar a otel din da ya sauka dake birnin Auckland, fadar mulkin kasar, kuma ya bayar da wani jawabi, 'yan siyasa da 'yan kasuwa da masana sama da 500 sun halarci bikin.
Yayin bikin, Li Keqiang ya bayyana cewa, tun bayan da aka kulla huldar diplomasiya kafin shekaru 45 da suka gabata, kasashen biyu suna gudanar da huldar yadda ya kamata, yanzu dai huldar ta kara kyautatuwa, har hadin gwiwa dake tsakanin sassa biyu ya kai matsayin koli a tarihi, kana har kullum New Zealand tana mai da hankali sosai kan huldar dake tsakaninta da kasar Sin. Li Keqiang ya yi nuni da cewa, kasar Sin tana son sanya kokari tare da New Zealand domin ciyar da tattalin arzikin duniya gaba, tare kuma da cimma burin samar da makomar bil Adama guda daya, da kara kyautata tsarin tafiyar da tattalin arzikin duniya yadda ya kamata.
Firayin minsitan New Zealand English ya bayyana cewa, ziyarar da Li Keqiang ke yi za ta sa kaimi kan ci gaban hulda da hadin gwiwa dake tsakanin kasashen biyu.(Jamila)