Bisa gayyatar da firayin ministan kasar New Zealand Bill English ya yi masa, firayin ministan kasar Sin Li Keqiang na gudanar da ziyarar aiki a kasar tsakanin ranakun 26 da 29 ga wata.
Yayin ziyarar, Li Keqiang ya gana da babban gwamnan New Zealand Patsy Reddy, kuma ya tattauna da takwaran na sa Bill English, inda suka yi musayar ra'ayoyi kan manyan batutuwan kasa da kasa da na shiyya shiyya da ke jan hankalinsu.
Shugabannin biyu sun jinjinawa sakamakon da suka samu yayin da suke kokarin gudanar da huldar dake tsakaninsu cikin shekaru 45 da suka gabata, wato tun bayan kulla huldar diplomsiyya tsakaninsu, kana sun amince cewa, za su kara karfafa cudanya ta hanyar kai wa juna ziyara, tare kuma da kara zurfafa zumuncin siyasa da hadin gwiwa da musayar al'adu bisa tushen nuna biyayya da moriyar juna.
Sun kuma yaba da sakamakon da suka samu a fannin hadin gwiwar tattalin arziki da ciniki, inda suka amince cewa, za su gudanar da shawarwari kan ciniki maras shinge tsakaninsu, kana za su kara mai hankali kan hadin gwiwa a fannonin aikin gona da kiwon dabbobi da gina manyan kayayyakin more rayuwar jama'a da kirkire-kirkiren kimiyya da fasaha, da al'adu da samar da ilimi da yawon bude ido da dai sauransu.
Baya ga haka, suna fatan kara karfafa hadin gwiwa a fannin shari'a domin dakile cin hanci da rashawa da laifuffukan dake shafar kasa da kasa.(Jamila)