in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Dakarun tsaron Pakistan sun hallaka 'yan ta'adda 108 a wani shirin yaki da ta'addanci
2017-04-18 13:14:24 cri

A jiya Litinin dakarun tsaron kasar Pakistan sun yi nasarar kashe 'yan ta'adda 108 a wani samame da suka kaddamar don yaki da ta'addanci wanda sojin kasar suka kaddamar da shi a watan Fabrairun bana.

Shirin yaki da ta'addanci mai taken "Radd-ul-Fasaad," ko kuma "Reject Discord" a turance, an kaddamar da shi ne bayan wasu jerin hare haren ta'addanci wanda aka kaddamar, lamarin da ya yi sanadiyyar hallaka mutane sama da 100 a fadin kasar.

Dakarun sojin kasar da sauran jami'an tabbatar da tsaron kasar sun yi hadin gwiwa don gudanar da shirin tare.

Da yake tsokaci game da sakamakon da aka samu na wannan shirin murkushe 'yan ta'addar, kakakin rundunar sojin kasar Manjo Janar Asif Ghafoor, ya shedawa taron manema labarai cewa, a kalla mutane 4,500 wadanda ake zargi ne ake tsare da su tun farkon kaddamar da shirin.

Ya ce za'a cigaba da gudanar da shirin, har sai an kammala kakkabe 'yan ta'addar baki daya.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China