in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Pakistan: An cafke mutane 5 da ake zargi da kai harin ta'addanci a Sindh
2017-02-20 10:29:10 cri

A jiya Lahadi ne shugaban hukumar 'yan sandan lardin Sindh da ke kudancin kasar Pakistan A.D Khawaja ya bayyana cewa, hukumar aiwatar da dokokin kasar ta cafke mutane 5 da ake tuhuma da hannu cikin harin ta'addancin nan na wurin addini da ya auku a lardin.

Jami'in ya kara da cewa, bisa bayanan da suka samu, hukumar aiwatar da dokokin kasar ta dauki matakai masu yawa tsakanin yankunan lardin Sindh da lardin Balochistan, inda sakamakon hakan aka kama mutane 3, wadanda ake zargi da ba da taimako wajen kai harin. Yanzu haka dai an kama jimillar mutane 5 bisa zargin kitsa wannan hari.

A daren ranar 16 ga watan nan ne dai aka kaddamar da harin na kunar bakin wake, a wani wurin ibada dake yankin Sehwan na lardin Sindh, wanda kuma ya haddasa mutuwar mutane a kalla 88, tare da raunatar wasu 343. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China