in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Pakistan ta bukaci Afghanistan da ta kama 'yan ta'adda 76
2017-02-17 20:20:21 cri

Rundunar sojan kasar Pakistan ta ce ta mikawa kasar Afghanistan wata takardar sunayen 'yan ta'adda, wadanda suke boye a Afghanistan, tana mai bukatar gwamnatin Afghanistan din da ta kama su, ta mika su a hannun Pakistan.

A jiya Alhamis ne dai hafsan-hafsoshin sojan kasa na Pakistan Qamar Javed Bajwa, ya fidda wata sanarwar dake cewa, masu adawa da Pakistan wadanda suke samun mafaka a Afghanistan ne suka kitsa jerin hare-haren ta'addanci a Pakistan a 'yan kwanakin baya bayan nan. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China