Bisa binciken da aka gudanar, an gano cewa, maharin ya yi ado irin na 'yan mata mazauna yankin, inda ya shiga wajen ibadar tare da tada bam din da ke jikinsa mai nauyin kilo 7.
Gwamnatin lardin Sind, ta ayyana ranar 17 zuwa 19 ga wata, a matsayin ranar zaman makoki, inda za kuma a yi kasa-kasa tutoci domin nuna alhinin mutuwar da kuma mutanen da harin ya rutsa da su.
Tun daga ranar 17 ga wata ne, aka fara aikin kama 'yan ta'adda a duk fadin kasar ta Pakistan, inda aka karfafa matakan tsaro, musamman a wasu wuraren da aka fi kai harin ta'addanci, sannan, za a rufe wuraren ibada cikin dan lokaci. (Maryam)