in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sudan za ta halarci taron AFRICOM a karon farko
2017-04-18 10:41:15 cri

Kakakin rundunar sojin kasar Sudan ya bayyana cewa kasar za ta halarci taron manyan hafsoshin soji na kasashen Amurka, Turai da Afrika wato (AFRICOM) a karon farko, wanda za a gudanar a Stuttgart, na kasar Jamus.

Babban jami'in dakarun sojin Sudan Emad Eddin Mustafa Adawi, shi ne zai jagoranci tawagar a lokacin wannan taro.

Cikin wata sanarwa da kakakin rundunar sojin ta Sudan Ahmed Khalifa Al-Shami ya fitar, ya ce, wannan mataki wata alama ce dake nunawa duniya cewar dage takunkumin da ka azawa kasar zai yi matukar tasiri wajen ba ta damar shiga harkokin kasa da kasa domin bada gudunmowa wajen yakar ayyukan ta'addanci, da yaki da kwararar bakin haure ta barauniyar hanya, da kuma yaki da yin almundahanar kudade.

Ya kara da cewa halartar taron wata 'yar manuniya ce dake jaddada irin kyakkyawar fahimtar dake tsakanin Sudan da Amurka da kuma yunkurin tabbatar da goge sunan kasar ta Sudan daga jerin sunayen kasashen da Amurka ta ayyana a matsayin masu tallafawa 'yan ta'adda, kana zai tabbatar da matakin da Amurkar ta dauka na dagewa Sudan takunkumin harkokin tattalin arziki.

Halartar taron da Sudan din za ta yi, ya biyo bayan cigaban dangantakar da aka samu ne tsakanin Sudan da Amurka a watan Janairun wannan shekara bayan da Amurkar ta ayyana dage takunkumin tattalin arzikin da ta azawa Sudan din tun shekarar 1993.

Har yanzu Sudan tana cikin jerin sunayen kasashen da Amurka ta ayyana a matsayin masu tallafawa 'yan ta'adda.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China