Mbeki, wanda shi ne shugaban tawagar aiwatar da shirin zaman lafiya na tarayyar Afrika a kasar Sudan wato AUHIP, ya fara ganawar ne da Ibrahim Mahmoud Hamid, mataimakin na musamman ga shugaban kasar Sudan kuma shugaban tagawar gwamnati don tattaunawar sulhu,
Bayan kammala tattaunawar, Hamid ya shedawa taron manema labarai cewa, an amince cewar AUHIP za ta ci gaba da daukar matakai wadanda za su tattabar da zaman lafiya a Sudan, kuma za'a shigar da kungiyoyin 'yan tawayen kasar cikin shirin tattaunawar sulhu na kasar.
Jami'in gwamnatin ta Sudan ya jaddada cewa, gwamnatin kasar a shirye take da amince da maido da tattaunawar sulhu tskaninta da 'yan tawayen na SPLM arewaci da masu dauke da makamai na yankin Darfur.
Mbeki ya ce a halin yanzu suna dakon martani daga bangaren kungiyoyin 'yan tawayen kasar domin sanya lokacin ci gaba da tattaunawar. (Ahmad Fagam)