Kwamitin kwararru masanan tsaro na Afrika wato CISSA, ya kuma bukaci a dinga musayar bayanai game da duk wata kungiya mai zaman kanta dake da mummunar manufa a fadin nahiyar.
Wakilai daga kasashe mambobin CISSA, da na kasa da kasa da shiyya shiyya, sun kammala wani taron karawa juna sani na shiyya shiyya na tsawon kwanki 3 a birnin Khartoum na kasar Sudan, domin tattaunawa game da batun tsaro da zaman lafiyar Afrika.
Mataimaki na farko ga shugaban kasa, kana firayiministan kasar Sudan Bakri Hassan Saleh, ya bayyana wannan taron a matsayin wani babbban buri na nahiyar Afrika, ya kara da cewa masu adawa da ci gaban bil Adama za'a iya yin galaba a kansu, ko na cikin gida ne ko kuma na kasashen waje ko kuma kungiyoyi masu zaman kansu masu mugaye manufofi.
A wani labarin kuma, babban sakataren CISSA, Shimelis Woldesemayat, ya ce za'a mai da hankali sosai kan barazanar masu shirya ta'addanci, da masu dauke da makamai da kungiyoyi masu mugayen manufofi. (Ahmad Fagam)