in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shirin "ziri daya da hanya daya" zai sa kaimi ga hadin gwiwa a tsakanin Sin da Najeriya
2017-04-17 13:18:53 cri

Za a kira taron dandalin tattaunawa kan hadin gwiwar kasa da kasa da shirin "ziri daya da hanya daya" za a gudanar a ranakun 14 da 15 ga watan Mayun bana a birnin Beijing na kasar Sin.

Taken dandalin tattaunawar shi ne "inganta hadin gwiwa tsakanin kasashe, don raya shirin 'ziri daya da hanya daya', a kokarin samun nasara da ci gaba na bai daya."

A yayin taron, ana sa ran tattaunawa kan yadda za a raya muhimman ababen more rayuwa na kasashen da abin ya shafa, da hadin gwiwar tattalin arziki da cinikayya, da zuba jari kan masana'antu, da raya makamashi, da goyon bayan juna ta fuskar hada-hadar kudi, da cudanyar al'adu, da kiyaye muhallin halittu, da ma hadin gwiwa ta fuskar teku.

Wane irin tasiri shirin "ziri daya da hanya daya" zai bayar ga hadin gwiwar Sin da Afirka, musamman ma ga tarayyar Najeriya, kuma kasashen biyu za su ci gajiya daga wannan shiri a wadannen fannoni? Game da wannan, wakiliyarmu a Abuja Amina ta samu damar zantawa da Farfesa Sheriff Ghali Ibrahim, wanda ke nazarin harkokin kasar Sin a Jami'ar Abuja ta Najeria.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China