Yawan jarin da Sin ta zuba ga kasashe da yankuan dake bin "Ziri daya da hanya daya" ya kai kashi 20 cikin dari na dukkan jarin da ta zuba ga kasashen waje
Kakakin ma'aikatar harkokin cinikayyar kasar Sin Shen Danyang, ya gabatar da alkaluman dake nuna cewa ya zuwa karshen watan Mayun bana, yawan jarin da Sin ta zuba ga kasashe da yankuna 64 dake bin "Ziri daya da hanya daya" ya kai dala biliyan 161.2, adadin da ya kai kashi 20 cikin dari, na daukacin jarin da Sin ta zuba ga kasashen waje.
Mr. Shen wanda ya bayyana hakan a jiya Talata, ya kara da cewa akwai alamu dake nuna cewa, kasashe da yankunan dake bin "Ziri daya da hanya daya" sun fara zama wuraren da kamfanonin Sin suke dora muhimmanci ga zuba jari a cikin su. (Zainab)