Kamfanin na Moody's wadda ya kasance daya daga cikin manyan hukumomin uku na duniya da ke kimanta matsayin ba da lamuni, ya kuma kiyasta cewa, wannan shiri zai kawo alheri ga kasashen da ke da karamin matsakaicin kudin shiga, wadanda kuma ba su iya warware matsalar gibin cinikayyar shigi da fici ta hanyar amfani da jarin ketare ba, baya ga gaza samun yawan masu zuba jari daga ketare.
Ban da wannan, kamfanin na Moody's yana ganin cewa, kasar Sin ita ma za ta ci gajiya sosai daga shirin na "ziri daya da hanya daya", wanda zai sa kaimi ga harkar zuba jari da kuma sassauta illar da tabarbarewar tattalin arziki ke haifarwa. A sa'i daya kuma, shirin zai kara karfafa aikin fitar da kayayyaki zuwa ketare, da kuma shigo da dimbin kayayyakin da Sin ke bukata, hakan zai iya kiyaye ci gaban karuwar tattalin arzikin kasar Sin.(Kande Gao)