Kasashen da ke kan tsarin nan na ziri daya da hanya daya, sun samu gagarumar riba daga jarin da suka zuwa a kasar Sin, cikin watanni 9 na farkon hada-hadar da aka gudanar.
Wata kididdiga da ma'aikatar cinikayyar kasar Sin ta fitar ta nuna cewa, a cikin shekara guda, kasashen sun shigar da jarin da yawan sa ya kai dalar Amurka biliyan 6.12, sun kuma ci ribar da ta kai kaso 18.4 cikin dari, a tsakanin watanni taran farko, wanda hakan ya dara koma bayan da aka samu na kaso 29.3, tsakanin watannin Janairu zuwa Agustan wannan shekara.
Kididdigar ta kuma nuna cewa, a bangarin harkokin ba da hidimar hada-hadar kudade, jarin da kasashen suka zuba ya rubanya har sau 15, yayin da fannin ba da haya, da bangaren hidimar kasawanci ya rubanya sama da sau 2. A cewar wannan kididdiga, kasashen Saudi Arabia, da Malaysia, da Singapore ne suka fi zuba jari a kasar ta Sin cikin watannin 9.
Wannan shiri na ziri daya da hanya daya, tsari ne na bunkasa tattalin arzikin kasashen duniya da dama, karkashin manufar hanyar raya tattalin arziki ta siliki ta karni na 21, da kuma hanyar siliki ta ruwa, wadda shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar a shekara ta 2013, da nufin farfado da cinikayyar kasashen dake kan tsohuwar hanyar siliki. Ya zuwa yanzu dai akwai sama da kasashe da yankuna 60, wadanda ke da al'ummu kusan biliyan 4.4 dake cikin wannan tsari.(Saminu)