Yawan jarin da Sin ta zuba ga kasashen dake cikin shirin "ziri daya da hanya daya" ya karu
Kakakin ma'aikatar kasuwanci ta kasar Sin Shen Danyang, ya ce kamfanonin Sin sun zuba jari kai tsaye ga kasashe 48 dake cikin shirin "ziri daya da hanya daya" a watanni 6 na farkon shekarar bana, wanda yawan sa ya kai dala biliyan 7.05, adadin da kuma ya karu da kashi 22.2 cikin dari bisa na makamancin lokaci a bara.
Karkashin hakan, yawan kayayyakin da Sin ta fitar zuwa kasashen dake cikin shirin na "ziri daya da hanya daya" ya karu da kashi 0.4 cikin dari bisa adadin dukkanin cinikayyar ta da sauran kasashen waje, yayin da yawan irin wadannan kaya da Sin ta fitar zuwa abokan cinikayyar ta banda yankin Hongkong, da Macau da Taiwan, ya karu da kashi 1.2 cikin dari. (Zainab)