in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Somaliya tana sa ran raya dangantakar dake tsakaninta da Sin
2017-04-16 13:24:56 cri
Bisa labarin da aka samu a ran 15 ga wata, an ce, shugaban kasar Somaliya Mohamed Abdullahi Mohamed, ya bayyana cewa, gwamnatin Somaliya tana mai da hankali kan raya dangantakar dake tsakaninta da kasar Sin, domin karfafa hadin gwiwar dake tsakanin kasashen biyu.

Bayan shugaba Mohamed ya karbi takardar wakilcin kasa da sabon jakadan Sin dake kasar Somaliya Qin Jian ya mika masa, ya bayyana cewa, kasar Sin tana baiwa Somaliya taimako da goyon baya cikin dogon lokaci da ya gabata, al'ummomin kasarsa suna yabawa kasar Sin,sannan ya nuna godiya ta musamman ga gwamnatin kasar Sin dangane da babban taimako da ta samarwa kasarsa, a yayin da ake fama da bala'in fari a kasar Somaliya.

Bugu da kari, ya ce, a halin yanzu, gwamnatin kasar Somaliya ta dukufa kan aikin sake gina kasa cikin yanayin zaman lafiya, yana fatan kamfanonin kasar Sin za su iya dawowa kasar Somaliya domin ba da gudummawa ga kasar kan wannan aiki.

A nasa bangaren, Qin Jian ya ce, gwamnatin kasar Sin tana son karfafa hadin gwiwar dake tsakaninta da gwamnatin Somaliya, domin cimma sakamako mai kyau ta hanyar hadin gwiwar tsakanin bangarorin biyu. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China