Wani jami'in dan sanda ya bayyana cewa dukkan jami'an 4, 'yan asalin kasar Somaliya ne, kuma suna aiki ne na rigakafin cutar polio a kasar ta Somaliya, karkashin shirin kiwon lafiya na MDD.
Jami'in, wanda bai amince a ambaci sunansa ba, ya tabbatar da cewa mayakan na A-Shabaab sun yi awon gaba da mutanen 4 ne a yankin Gedo a lokacin da suke yin bulaguro a kusa da garin Luuq.
Ya ce tuni aka fara tattaunawa domin cimma matsaya don a sako jami'an agajin su 4, inda wasu dattawa a yankin suke shiga tsakani domin a warware matsalar. Sai dai kawo yanzun babu wani karin haske daga hukumar ta WHO.
Kungiyar masu tsattsauran ra'ayin Islama ta Al-Shabaab mai fafutukar kifar da gwamnatin Somaliya mai samun goyon bayan kasashen yammaci, ba wannan ne karon farko da kungiyar ke kaddamar da hari kan jami'an ba da agaji na kasa da kasa ba, a lokutan baya ma, kungiyar ta sha yin garkuwa da jami'an domin neman kudaden fansa. (Ahmad Fagam)