in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Tashin Bam ya hallaka mutane 6 a birnin Mogadishu
2017-04-05 18:58:28 cri
Wani Bam da aka dana jikin wata mota ya tarwatse kusa da wasu ma'aikatun gwamnatin Somaliya biyu dake birnin Magadishu a Larabar nan, in da nan take mutane 6 suka rasa rayukan su, yayin da kuma wasu mutanen 10 suka jikkata.

Da yake tabbatar da aukuwar lamarin, jami'in 'yan sandan yankin Ahmed Elmi, ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, Bam din ya tarwatsa motar da yake ciki, a kusa da wani gidan cin abinci dake daura da ma'aikatar wasanni, da ta tsaron kasa dake kusa da juna, a gundumar Shangani dake birnin na Mogadishu.

Shi ma kakakin gwamnatin yankin Benadir Abdifitah Omar Halane, ya tabbatar da aukuwar harin, sai dai a cewar sa mutane 5 ne suka rasu. Halane ya ce jami'an tsaro na duba yadda al'amarin ya auku, da nufin damke wadanda ke da hannu a kitsa shi.

Kawo yanzu dai ba wata kungiya da ta dauki alhakin kaddamar da wannan hari. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China