in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Firaministan Somaliya ya sanar da sunayen sabbin ministoci
2017-03-23 10:56:19 cri
Firaministan kasar Somaliya Hassan Ali Khaire ya sanar da sunayen sabbin ministocinsa, ciki har da mataimakin firaminista da ministoci 26 da sakatarorin harkokin cikin gida 15, da kuma mataimakan minista 26.

Mr.Khaire ya bayyana cewa, sabbin ministocin za su yi kokarin sauke nauyin al'umma dake wuyansu tare da bauta wa kasar.

Ya kuma kalubalanci majalisar dokokin kasar da ta gaggauta bincike da kuma zartas da jerin sunayen, ta yadda majalisar ministocin za ta fara aiki da wuri.

Shugaban Somaliya Mohammed Abdullahi Mohammed, ya yi maraba da yadda aka bayyana sunayen sabbin ministoci, yana mai cewa, zai gudanar da harkokin mulkin kasar tare da ministocin, domin kiyaye moriyar al'umma.

A ranar 1 ga watan nan ne, majalisar dokokin kasar Somaliya ta kada kuri'a, inda aka nada Hassan Ali Khaire a matsayin sabon firaministan kasar.(Lubabatu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China